Hafsat Nasir Umar
Kamfanin hakar danyen man fetur na Shell zai biya diyyar dala miliyan 16 ga wasu manoma a yankin Neja-Delta.
Hakan na cikin diyyar da kamfani zai biya ga waɗanda malalar man fetur ta yi musu barna a gonakinsu.
Alkawarin biyan diyyar na kunshe cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a tare da hadin gwiwar reshen cibiyar Friends of the Earth a kasar Netherlands.
Matakin ya biyo bayan hukuncin kotun Netherlands inda ta kama reshen kamfanin na Shell a Najeriya da laifin malalar mai a shekarar da ta wuce kuma ta umarci Shell ya biya diyya.
Tun a shekarar 2008 ne manoma daga Neja-Delta tare da taimakon kungiyar kare hakkin bil adama ta Friends of the Earth suka gurfanar da Shell a gaban kotun da ke The Hague sakamakon gurbata musu muhalli da ya yi a tsawon shekarun da ya shafe yana hako albarkatun fetur a yankin.
Kamfanin Shell ya yi barnar a shekarun 2004 zuwa 2007.