Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiPeter Obi yayi ganawar sirri da Good luck Jonathan

Peter Obi yayi ganawar sirri da Good luck Jonathan

Date:

Hafsat Nasir Umar

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi ya gana da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a gidansa da ke birnin Yenagoa a jihar Bayelsa.

 

Wannan ganawa tsakanin biyun ta kasance ta sirri gabanin fara gangamin kamfen na jam’iyyar LP a jihar Bayelsa.

 

Tsohon shugaban kasa Jonathan, ya ce a halin yanzu Najeriya na cikin matsanancin halin rabuwar kai, inda yace idan Peter Obi ya samu nasara a zaben badi ya fara da hada kan Najeriya.

 

Hakazalika, ya yaba wa Obi bisa daukar matakin tsayawa takara a zaben na badi.

 

Peter Obi ya samu rakiyar abokin takararsa, Yusuf Baba-Ahmad da wasu jiga-jigan jam’iyyar.

Latest stories

Related stories