Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAmbaliya:Gwamnatin tarayya ta bukaci a rufe gadar Tiga

Ambaliya:Gwamnatin tarayya ta bukaci a rufe gadar Tiga

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Gwamnatin Tarayya ta bukaci Gwamnatin Kano ta rufe Gadar Sarkin Kogi da ke Tiga a Karamar Hukumar Bebeji gaba daya domin kare rayukan masu ababen hawa da sauran jama’a.

 

Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu, ya yi kiran ne a lokacin ziyarar gani da ido a Madatsar Ruwa ta Tiga

da ta Bagauda tare da Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

 

Sanarwar da Gwamnatin Jihar Kano ta fitar ta hannun kakakin mataimakin gwamnan jihar, Hassan Fagge, ta ruwaita ministan na cewa sabanin ji-ta-ji-ta da ake yadawa, magudanan ruwan madatsan ruwan biyu suna aiki yadda ya kamata.

 

Ministan ya kara da cewa babu inda ambaliya ta shafi madatsan ruwan biyu sannan yawan ruwansu bai karu ba, kamar yadda ake yadawa.

 

Don haka ya umarci Hukumar Kula da Kotun Hadejia Jama’are River da ta ci gaba da ayyukan gyara na yau da kullum da ta saba a madatsan ruwa biyu.

 

Ganduje, wanda mataimakinsa, Nasiru Gawuna, ya wakilata ya ba da tabbacin Gwamnatin Kano na ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.

 

Ya kuma bayyana ziyarar ministan, wanda ya ce an yi a kan lokaci a matsayin alamar kulawar Gwamnatin Tarayya da Shugaba Muhammadu Buhari, da abin da ya shafi mutanen Kano.

 

A makon jiya dai Madatsar Ruwa ta Tiga ta yi ambali ya tare da lalata gonaki da gidaje da hanyoyi, baya ga raba mutane da dama da muhallansu.

Latest stories

Related stories