33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiNCAA ta dakatar ta jirgin Azman daga aiki

NCAA ta dakatar ta jirgin Azman daga aiki

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa ta dakatar da kamfanin jirgin  Azman daga aiki sakamakon kin sabunta shedar lasisinsa

Hakan na zuwa ne ‘yan watanni kadan, bayan Dana Air da Aero Contractors suma aka dakatar da su sakamakon matsaloli da suka fuskanta a kan jiragen su.

An bayyana cewa da sanyin safiyar ranar Alhamis ne mahukuntan kamfanin na Azman Air suka ce ma’aikatansu kar su fito bakin aiki, saboda dalilan gudanar da aiki.

A farkon wannan shekarar, yayin da daya daga cikin tarukan da hukumomin gwamnati da kamfanonin jiragen sama suka yi, hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa ta bayyana cewa, kamfanonin jiragen na bin bashin Naira biliyan 42 da dala miliyan 7.8.

Musa Nuhu, Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA), bayan taron ya bayyana cewa, kamfanonin jiragen za su rika fitar da kudade a kowane wata, domin biyan basussukan da ake bin su, ko kuma su fuskanci matsala idan ba su sabunta takardar shaidar lasisin su ba ta Air Operators (AOC).

Latest stories