Saurari premier Radio
21.8 C
Kano
Saturday, March 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda wani matashi ya mutu a kududdufi a Kano

Yadda wani matashi ya mutu a kududdufi a Kano

Date:

Wani matashi dan shekara 17  Suleiman Muhammed, ya nutse a cikin wani kududdufi dake unguwar Wailari ta karamar hukumar Kumbotso a nan jihar Kano.

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar a ranar Laraba a nan  Kano ya ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

Kakakin hukumar ya ce an fito da matashin daga cikin  ruwan a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwarsa.

Ya kuma baiyana cewa  lamarin ya samo asali ne bayan da matashin ya je  kududdufin domin yin ninkaya.

Abdullahi ya ce an mika gawar  marigayin ga mai unguwar  Wailari Magaji Adamu inda aka yi masa sutura.

Latest stories

CBN Ya Kwace Lasisin Yan Canji Sama da Dubu Hudu A Faɗin Nijeriya

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da soke lasisin...

Dangote ya bayar da shawarar mayar da kasuwar waya ta Farm Center zuwa cibiyar fasaha

Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote, ya shawarci jami'ar...

Related stories