Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari zai gabatar da kasafin kudin badi

Buhari zai gabatar da kasafin kudin badi

Date:

Majalisar wakilai ta ce shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin badi a makon farko na watan Oktoba.

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya bayyana hakan  lokacin da yake yiwa manema Labarai  jawabi, jim kadan bayan kammala  duba  dakunan taron  sauraron ra’ayoyin  jama’a  na  28 da kuma  234  da  majalisar za ta yi amfani dasu.

Majalisar za ta yi afani da zaueuka ne na wucin gadi  don  gudanar da zamanta na yau da kullum, sakamakon gyare-gyaren da ake kan yiwa zauren majilar a halin yanzu.

Yace  za’a kammala saita wurin da majalisar  za ta rika amfani dashi a matsayin zauren ta na wucin gadi gabanin ranar  20 ga watan da muke ciki, lokacin da majalisar  zata koma bakin aiki.

Femi Gbajabiamila ya kara da cewa, aikin gyara majalisar zai fi amfanar  sabbin yan majalisa masu zuwa  kasancewar  ba zai kammala ba har cikin watan Augustan badi.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...