Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn sauyawa jami’ar Wudil suna zuwa jami’ar Aliko Dangote

An sauyawa jami’ar Wudil suna zuwa jami’ar Aliko Dangote

Date:

Aminu Abdullahi Ibrahim

 

Majalisar dokokin Kano ta amince da sauya wa jami’ar Kimiyya da Fasaha ta garin Wudil suna zuwa Jami’ar Kimiyya da fasaha Aliko Dangote.

 

Majalisar ta amince da hakan ne a zamanta na ranarTalata, bayan da ta amince da rahoton kwamitinta na harkokin ilimi mai zurfi kan gyaran dokar jami’ar.

 

Shugaban kwamitin Alhaji Ali Ibrahim Isah wakilin ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono ne ya gabatar.

 

A zantawarsa da manema labarai, Ali Ibrahim Isah Shanono, ya ce, za a sauya sunan jami’ar ne la’akari da irin gudunmawar da Alhaji Aliko Dangote ke bayarwa a ƙasar nan musamman ma ta fannin ilimi.

 

A wani labarin kuma, majalisar ta karɓa tare da amincewa da rahoton kwamitinta na harkokin wasanni kan matsalolin da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta tsinci kanta a ciki a baya-bayannan.

 

Kwamitin ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin harkokin wasanni na majalisar Nuruddeen Alhassan Ahmad, ya ce, binciken da suka gudanar ya gano cewa, ƙungiyar ta Kano Pillars tana fama da rikicin cikin gida tare da bin bashin fiye da Naira miliyan ɗari da kuma sauran matsaloli da suka dabai baye ta.

Latest stories

Related stories