30.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKotu ta baiwa DSS damar ci gaba da tsare Mamu har watanni...

Kotu ta baiwa DSS damar ci gaba da tsare Mamu har watanni biyu

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Mukhtar Yahya Usman

 

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta amincewa hukunar DSS ta tsare Tukur Mamu har tsawon watanni biyu.

 

Mai Shari’a Nkeonye Maha ne ya bayar da umarnin a zaman kotun ranar Talata.

 

Lauyan hukumar DSS Ahamad Magaji ne ya roki kotun a madadin hukumar da abasu damar ci gaba da tsare Mamun domin fadada bincike.

 

Bayan rokon ne kuma kotun ta baiwa hukumar dama da ta ci gaba da tsare shi har tsawon watanni biyu.

 

Idan za a iya tunawa a ranar 6 ga watan nan ne jam’ian yan sandan kasa da kasa suka kama shi a filin jirgin saman Alkahira da ke Masar.

Daga baya kuma aka dawo dashi nan gida Najeriya inda yan sandan na DSS Suka ci gaba da tsare.

Latest stories