Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZabar PDP a Katsina jihadi ne-Lado Dan Marke

Zabar PDP a Katsina jihadi ne-Lado Dan Marke

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Dan takarar gwamnan Jihar Katsina a zaben 2023, Sanata Yakubu Lado Danmarke, ya ce jihadi ne a mara wa jam’iayr PDP baya ta lashe zabukan 2023 a halin da ake ciki a jihar.

 

Lado ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a Karamar Hukumar Safana ta jihar, yayin karbar sabbin ’yan jam’iyar da suka sauya sheka daga wasu jam’iyyu a jihar.

 

Lado ya ce ko shakka ba ya yi cewa PDP za ta samu nasara a 2023 a Jihar Katsinan da tazara mai yawa.

 

“Mu a nan Katsina, ba mu da wata baraka ko rarrabuwar kai a PDP.

 

“Na fafata da ’yan takara hudu a zaben fitar da gwanin jam’iyyar da aka gudanar watannin baya, inda na yi nasara.

 

“Yanzu haka daya daga cikinsu ne abokin takarata, sai na ukun da ya koma takarar dan Majalisar Tarayya, na hudun kuma yana tare da mu ta hanyar bayar da shawarwari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.”

Latest stories

Related stories