Gwamnatin tarayya ta ce ta sanya hannun kan wata yarjejeniya da kasar Amurka kan yadda za a dawo da Dala Miliyan 23 da wasu shugabannin kasar nan suka sace.
Cin wadanda ake zargi da sa ce kudin suka kuma boye a kasar ta Amurka harda tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha.
Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya sanya hannun a madadin Gwamnatin Tarayya, yayin da Jakadan Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, ya sanya hannu a madadin gwamnatin Amurka.
Malami ya ce idan aka ƙwato kuɗaɗen za a yi amfani da su wajen samar da ababen more rayuwa.
A cewarsa, gwamnatin tana nan tana ƙoƙari don dawo da kuɗaɗen da aka sace.