Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Friday, April 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBa mu karbi tuban Turji ba har sai ya ajiye makamai-Gwamnatin Zamfara

Ba mu karbi tuban Turji ba har sai ya ajiye makamai-Gwamnatin Zamfara

Date:

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce na za ta yarda cewa Bello Turji ya tuba ba har sai ya ajiye makamansa.

Wannan na fitowa ne ta bakin shugaban kwamitin kwance damarar ’yan bindiga a jihar Abdullahi Shinkafi, ranar Talata.

Ya ce ba zai shiga wata tattaunawa da ‘yan bindiga ba, domin yawancinsu ba su da gaskiya.

Wannan dai na zuwa ne bayan shekaru biyu da bullo da shirin sulhu da ’yan bindiga.

Amma hakan bai hana wasu daga cikinsu komawa daji tare da daukar makamai ba.

A ranar Asabar da ta gabata ne Mataimakin Gwamnan jihar, Hassan Nasiha ya sanar cewa, Turji ya rungumi shirin tattaunawar zaman lafiya.

Haka kuma ya yi alwashin fara kaddamar da farmaki kan sauran ‘yan bindiga a yankin Shinkafi da ke jihar.

Mataimakin gwamnan ya ce tun bayan da suka cimma matsaya game da tuban dan bindigar, yanzu fiye da makonni shida ke nan ba a sami asarar rai ba da ya danganci ayyukan ’yan ta’adda a jihar.

A yanzu haka dai Turji ya sanar da bukatar a sako masa ’yan bindigar da ke hannun gwamnati da kuma kawo karshen kisan da ya ce ana yi wa fulani ’yan uwansa.

A watan Yunin da ya gabata ne Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya umurci mataimakinsa da ya jagoranci tattaunawar sulhu da ’yan bindigar.

Wannan na zuwa ne matsayin yunkurin gwamna Matawalle na ribatar shirin rungumar sulhu da ‘yan bindigar.

A shekarar 2020 ce Gwamnatin Zamfara ta bullo da shirin sulhun a matsayin hanya daya tilo ta kawo karshen hare-haren ’yan bindigar da suka dauki tsawon shekaru 10 suna kaddamar wa al’umma tare da sace shanu baya ga garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.

An dai samu wasu daga cikin jiga-jigan ‘yan bindiga da suka mika kansu ga hukuma kamar irinsu Auwalun Daudawa wanda ya kitsa sace daliban makarantar Kankara da ke jihar Katsina a cikin watan Disamban 2020, inda har ya ajiye makamansa a bainar jama’a.

Latest stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...