Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAnshiga rudani kan batun daukar sabbin yan sanda a Najeriya.

Anshiga rudani kan batun daukar sabbin yan sanda a Najeriya.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Wata dambarwa ta kunno kai tsakanin rundunar yan sanda ta kasa da kuma hukumar Kula da ayyukan yan sanda.

 

Wannan ya biyo bayan hukumar kula da ayyukan yan sandan ta kasa ce dai ta sanar da dakatar da batun daukar sabbin jami’an.

 

Sanarwar na zuwa ne kasa da kwana guda da babban Sufeton yan sanda Usman Alkali Baba, ya nuna bacin ransa kan tallan da hukumar kula da ayyukan yan sanda tayi na neman masu sha’awar aikin dan sanda su mika bukatarsu ta shafinta na Internet.

 

Sai dai shugaban yan sanda na kasa ta bakin maimagana da yawun rundunar yan sandan Olumuyiwa Adejobi, ya nemi alumma suyi watsi da wannan talla.

 

A nasa bangaren mai magana da yawun hukumar kula da ayyukan yan sanda na kasa Ikechukwu Ani ya tabbatar da batun samun sabani tsakanin hukumarsu da rundunar ‘yan sanda ta kasa, sai dai yace za’a warware sabanin.

 

A shekarun bayama dai an taba samun makamancin wannan sabani tsakanin hukumar kula da ayyukan yan sandan ta kasa, inda kowa yake ikirarin shine yake da ikon daukar ma’aikata wato tsakanin hukumar ta kula da yan sanda da kuma rundunar yan sanda ta kasa.

 

Yanzu dai wannan sabani da akeyi ya jefa yan Najeriya cikin rashin tabbas kan batun daukar sabbin jami’an yan sanda da aka fara tun da farko.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...