Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan sanda sun kama barayin mutane 18 a Benue.

Yan sanda sun kama barayin mutane 18 a Benue.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

An kama wasu mutane 18 da ake zargi da laifin satar jama’a tare da kwace makaman da aka samu a wajensu.

 

Daga cikin makaman da aka kamasu dasu akwai bindiga guda daya kirar AK-47 da bindigogi kanana guda biyu da tarin alburusai.

 

Kakakin rundunar yan sanda na jihar Benue Catherine Anene Sewuese ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.

 

Sanarwar tace mutanen da ake zargin sun yi kokarin guduwa a wani shingen bincike na ‘yan sanda dake karamar hukumar Utonkon ta jihar.

 

Tuni dai aka fara bincike kan wadanda ake zargi da aikin satar mutanen da aka kama da yanzu haka suke hannun yan sanda.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories