Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHaya nake biya a gidan da nake zama a Abuja -Shekarau.

Haya nake biya a gidan da nake zama a Abuja -Shekarau.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Tsohon gwamnan Kano kuma sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau yace har yanzu haya yake biya a gidan da yake zama a birnin tarayya Abuja.

 

Shekarau ya bayyana haka a taron shura da ya gudanar a gidansa dake Mundubawa.

 

Yana wannan kalamai ne a matsagin martani kan wasu bayanai da aka yada cewar an masa tayin makudan kudde don ya sauya sheka daga jamiyyar NNPP.

 

Shekarau yace bai taba mallakawa kansa fili ba a tsahon shekaru 8 da tlyaui a matsayin gwamnan Kano

 

Yace duk wanda ya nuna wani gida da ya mallaka bayan wanda yake ciki da tsarin dokar jihar Kano ya bashi damar mallaka bayan kammala gwamnan to yaje ya bar masa.

 

Ya kuma ce hatta gidan da yake zama a birnin tarayya Abuja har yanzu kudin haya yake biya.

 

Wadannan kalamai na shekarau na zuwane bayan da ake rade-radin cewar zai sauya sheka zuwa jamiyyar PDP daga NNPP sakamakon rashin adalcin da suke zargin anyi musu a jamiyyar da tsohon gwamnan Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...