33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiGwamnatin tarayya zata soke kungiyar ASUU

Gwamnatin tarayya zata soke kungiyar ASUU

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Wasu rahotannin na cewar gwamnatin tarayya na duba yuwuwar soke kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU idan ta ki amincewa ta janye yajin aikin da takeyi.

 

Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Vanguard cewa ma’aikatar Ilimi ta kasa zata iya soke kungiyar ta ASUU muddin kungiyar malaman ta ki nuna dattaku kan kokarin da gwmnatin tarayya ke yi don warware matsalolin ilmin jamia a kasar nan.

 

Haka kuma gwamnatin tarayya ta amince a sanya biliyan 100 ga sha’anin ilimin jami’a dama wasu karin kudde don magance matsalolin da ake fuskanta a bangaren.

 

Wannan dai na zuwane bayan kungiyar ASUU ta tsunduma yajin aiki a ranar 14 ga watan Fabrairun.l, yajin aikin da yaki ci gaki cinyewa har yazuwa yanzu.

Latest stories