24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKasuwanciNajeriya za ta dawo da Dala miliyan 23 da aka sace aka...

Najeriya za ta dawo da Dala miliyan 23 da aka sace aka boye a Amurka

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Gwamnatin tarayya ta ce ta sanya hannun kan wata yarjejeniya da kasar Amurka kan yadda za a dawo da Dala Miliyan 23 da wasu shugabannin kasar nan suka sace.

Cin wadanda ake zargi da sa ce kudin suka kuma boye a kasar ta Amurka harda tsohon shugaban kasa Janar Sani Abacha.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya sanya hannun a madadin Gwamnatin Tarayya, yayin da Jakadan Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard, ya sanya hannu a madadin gwamnatin Amurka.

Malami ya ce idan aka ƙwato kuɗaɗen za a yi amfani da su wajen samar da ababen more rayuwa.

A cewarsa, gwamnatin tana nan tana ƙoƙari don dawo da kuɗaɗen da aka sace.

Latest stories