Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Wednesday, May 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciChina za ta yafewa kasashen Afrika 17 bashi

China za ta yafewa kasashen Afrika 17 bashi

Date:

Kasar China ta ce za ta yafe wasu basukan kudi marasa ruwa 23 da take bin wasu kasashen Afirka 17.

Kasar ta kuma bayyana aniyar ta na ba da taimakon abinci ga al’ummomin da ke fafutukar yadda zasu rayu.

Ministan harkokin wajen Kasar China Wang Yin ne ya bayyana hakan yayin jawabinsa a taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Kasar China da Afirka.

Ya ce matakin ya nuna aniyar kasar na kara karfafa dangantakar tattalin arziki da nahiyar Afirka.

Sai dai ministan ya ki bayyana kasashen da ake bi bashin ko adadin rancen.

Wani bangare na jawabin ya kuma ce, China za ta fadada shigo da kayayyaki daga Afirka.

“Za kuma mu ci gaba da kara yawan shigo da kayayyaki daga Afirka, da tallafawa bunkasar ayyukan noma da masana’antu na Afirka, da fadada hadin gwiwa a masana’antu masu tasowa” in ji sanarwar.

Kazalika, bisa kudurin da ta yi na yin hadin gwiwa tare da kasashen Afirka, China ta ce za ta sake tura dala biliyan 10 zuwa Afirka ta karkashin asusun bada lamuni na duniya IMF

Latest stories

Mamakon ruwa a Filato ya lalata gidaje, makarantu da asibitoci.

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya...

Related stories

Mamakon ruwa a Filato ya lalata gidaje, makarantu da asibitoci.

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya...