Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDole ne a hukunta wadanda suka kashe gwani Aisami-Bala Lau

Dole ne a hukunta wadanda suka kashe gwani Aisami-Bala Lau

Date:

Ƙungiyar Izala ta yi kira ga hukumomin ƙasar nan da su gaggauta gudanar da binciken ƙeƙe-da-ƙeƙe tare da tabbatar da ganin sun hukunta duk masu hannu a kisan gillar da aka yi wa fitaccen malamin nan na Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.

An kashe malamin ne a ranar Jumma’a, inda rundunar ‘yan sandan jihar Yobe ta tabbatar da cewa wasu sojoji biyu ake zargi da kisansa.

Shugaban ƙungiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya shaida wa BBC cewa kisan da aka yi wa malamin ta’addanci ne babba a kan al’ummar musulmi baki daya.

“A duk lokacin da aka rasa wani malami jigo, to an yi babbar asara ce ga al’umma baki daya.”

Sheikh Bala Lau ya ce abin takaicin shi ne hanyar da aka bi wajen kisan malamin, domin hanya ce da kowanne musulmi zain una bakin cikinsa da alhininsa kan abin da aka aikata don kisan gilla ne.

“Mu a matsayinmu na wannan kungiya, to muna kira ga gwamnatin tarayya a kan ta dauki mataki wurin gano da kuma daukar mataki kan wadanda suka aikata wannan ta’addanci kuma menene manufarsu? Kuma me ake so a jefa wa alumma?”.

“Wannan kisa ba za mu bari ba kuma ba za mu yi shiru ba za mu ci gaba da neman hakkin wannan malami.”

Shugaban kungiyar Izalar ya ce suna so a dauki matakin da ya dace bisa la’akari da dokokin kasa da kasa.

Latest stories

Related stories