Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRashin Tsaro: An gudanar da sauka 2,444 a Kano.

Rashin Tsaro: An gudanar da sauka 2,444 a Kano.

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Mahaddata alkur’ani da dama ne suka hadu a masallacin juma’a na Sheikh Ishaq Rabiu da ke Goron Dutse domin yiwa kasa addua saboda matsalar tsaro.

Malaman sun gudanar da sauka 2,444 tare da addu’ar neman zaman lafiya a Kano da ma kasa baki daya.

An dai gudanar da taron addu’ar ne karkashin jagorancin Khalifa Nafi’u Ishaq Rabiu.

Da yake jawabi Jim kadan bayan Kammala karatun, gwani Yusuf Ishaq Rabi’u ya ce babu wata matsala da za ta tunkari jama’a da alkur’ani ba zai magance ta ba.

A don hakan ne ma ya bukaci masu hannu da shuni da ‘yan siyasa su dinga shirya irin wadannan taruka domin nemawa kasa zaman lafiya.

Ya kuma godewa malaman da suka gabatar da sauka tare da  bawa al’umma ƙarfin gwiwar cewa Allah zai karbi bukatunsu.

Latest stories

Related stories