27.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiAlbarkacin ranar matasa ta duniya: Wata cibiya a Kano ta shirya horas...

Albarkacin ranar matasa ta duniya: Wata cibiya a Kano ta shirya horas da matasa 150 sana’o’in dogaro dakai kyauta

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Shehu Usman Salihu

 

Cibiyar bayar da horon sana’o’i ta SKH Vocational Training Development dake Kano, ta shirya bayar da horon kananan sana’oin dogaro dakai kyauta ga matasa 150, la’akari da matsin tattalin arzikin da yayi katutu tsakanin matasa.

 

Wannan dai bangare ne na tagomashin ranar matasa ta duniya da akai bikinta a juma’ar da ta gabata.

 

A zantawar ta da Premier radio cikin shirin matasa a premier na yammacin asabar din nan, shugabar kungiyar Haulat kabir Aliyu, ta ce halin matsin rayuwa da ake ciki hadi da rashin ayyukan yi tsakanin matasa, shi ne ya sanya su samar da shirin.

 

“Da naira 500 mutum zai iya fara sana’ar hada turaren kamshi dana fesawa a jiki ko daki ko sunadarin wanki da wanka, shi yasa zamu koyar da su kananan sana’o’i makamantan wadan nan” a cewar Haulat Kabir

Haulat Kabir ta kara da cewa “cikin makonni hudu zamu koyar da su, kuma su koya su dogara da kansu”.

 

A kowace shekara dai majalisar dinkin duniya kan fitar da take domin yin bikin ranar matasan, taken na wannan shekarar shi ne “bada goyon baya ga matasa’’.

Latest stories