Aba Dauda Abba
Kamfanin jirgin sama na AZMAN AIRLINE yace ya samu nasara a jigilar aikin hajjin bana na shekarar 2022.
Alkaluman da kamfanin ya fitar, ya nuna cewa yayi jigilar maniyyata dubu 7 da dari 300 wanda rundunar soji da hukumar NAHCON ta warewa kamfanin daga jihohi 16 na kasarnan.
Mataimakin Manaja kan sha’anin aikin Hajji na kamfanin jiragen saman Azman, Nuraddeen Aliyu ne ya shaida haka a wata ganawa da Premier Radio.
A cewarsa, duk da cewa sun samu kansu a ƙurarren lokaci, amma sun sami nasarar jigilar dukkan fasinjojin nasu.
Ya kuma ce sun dauki Alhazan jirgin yawo kimanin dubu 2 da dari 500 kuma sun yi hulda dasu cikin aminci, kuma sun kai su sun kuma dawo dasu akan lokacin da suka dauka.
Kazalika, alhazan sun fito ne daga jihohin Sokoto da Kebbi da Gombe da Bauchi da Borno da Kaduna da Yobe, da kuma nan jihar Kano.