Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBuhari ya sake nada Bashir Ahmad Hadiminsa

Buhari ya sake nada Bashir Ahmad Hadiminsa

Date:

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sake naɗa tsohon mai ba shi shawara, Bashir Ahmad, a matsayin mataimaki na musamman kan kafofin sadarwa na zamani.

Sakataren Gwamnati Boss Mustapha ne ya tabbatar da naɗin cikin wata wasiƙa da ya aika wa Bashir mai kwanan wata 20 ga Yuli.

A cikin wasiƙar, Mista Mustapha ya ce naɗin ya fara aiki ne tun ranar 19 ga watan na Yuli.

Bashir ya sauka daga muƙaminsa na mai ba wa shugaban ƙasa shawara sakamakon umarnin da fadar gwamnatin ta bai wa masu son neman takara a babban zaɓen 2023 da su ajiye muƙaman nasu.

Sai dai matashin ɗan asalin Jihar Kano ya yi rashin nasara a zaɓen fitar da gwani a ƙarƙashin jam’iyyarsu ta APC inda ya nemi takararar ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Gaya/Ajingi/Albasu daga Kano.

Bashir ya yi ƙorafin an yi maguɗi a zaɓen kuma ya bayyana cewa ya kai ƙara kotu don a bi masa haƙƙinsa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...