Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiSERAP ta yi barazanar maka INEC a kotu kan rajistar katin zabe

SERAP ta yi barazanar maka INEC a kotu kan rajistar katin zabe

Date:

Ƙungiyar SERAP ta buƙaci shugaban hukumar zabe  INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya tsawaita wa’adin rajistar katin zaɓe ko ta maka shi kotu.

Ƙungiyar ta yi wannan kira ne a wata wasika da mataimakin shugabanta, Kolawole Oluwadare ya fitar a jiya Asabar.

Serap ta bukaci INEC ala tilas ta bai wa ‘yan Najeriya miliyan 7 da suka yi rajista a intanet damar kamala cike ka’idar mallakar katin, domin tabbatar da cewa sun yi zabe kamar yada dokar kasa ta ba su ‘yan ci.

INEC ta bayyana cewa cikin ‘yan Najeriya 10,487,972 da suka yi rajistar katin zabe ta intanet, mutum 3,444,378 ne kawai suka samu damar karban katinsu.

Abin da SERAP ke cewa hakan na nufin kashi 32.8 cikin 100 ne kawai suka kammala matakan samun katin zabe.

SERAP ta ce akwai bukatar ayi wa mutane uzuri la’akari da kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta a cibiyoyin karban kati a sassan Najeriya.

Ƙungiyar ta ce idan ba a ɗau matakin gyara wannan tsari ba, to ‘yan Najeriya da dama za a danne musu hakki na jefa kuri’a.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories