Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanni'Yar wasan Najeriya Tobi Amusan ta sake lashe zinare a gasar commonwealth

‘Yar wasan Najeriya Tobi Amusan ta sake lashe zinare a gasar commonwealth

Date:

Yar wasan mata ta Najeriya Tobi Amusan ta sake lashe zinare a tseren mita 100 na gasar kasashen rainon Ingila wato (Commonwealth) da ke guna a birnin Birmingham na kasar Ingila.

 

Mai shekara 25 ta lashe zinaren ne a wasan da ta yi a ranar Asabar 6 ga Agustan da muke ciki.

 

Wannan na zuwa ne bayan da ta zama yar wasan Najeriya ta farko da ta lashe zinare a gudun mita 100 a gasar da ake ci gaba da gudanarwa.

 

Amusan, wacce ta shafe tarihin duniya a wasan kusa dana karshe, inda ta yi dakika 12.12, ta kuma hau kan layi a filin Hayward a dakika 12.06.

 

‘Yar kasar Jamaica Britany Anderson ta samu azurfa a dakika 12.23, yayin da zakaran Olympic Jasmine Camacho-Quinn ta Puerto Rico ta samu tagulla a 12.23.

 

Amusan ta kafa tarihi a duniya a wasan dab da na kusa da na karshe, inda ta karya mafi kyawun dakika 12.20 da Keni Harrison na Amurka ya yi a shekarar 2016.

 

Tawagar dai na kunshe da ‘yan wasa hudu ta Tobi Amusan, da Rosemary Chukwuma, da Grace Nwokocha da kuma Favour Ofili.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...