A ranar Juma’ar nan 05 ga Agustan shekarar da muke ciki, za’a fara gasar Firimiya ta kasar Ingila ta kakar wasannin shekarar 2022/2023 inda Arsenal da Crystal Palace zasu bude fagen gasar.
Filin wasa na Selhurst Park mallakin Crystal Palace ne zai karbi bakuncin fafatawar da kafin fara wasan zaá gudanar da kasai taccen biki.
Manchester City ce dai itace ke rike da kofin bayan lashewa da tayi sau biyu a jere a 2020/2021 da kuma 2021/2022.
Jadawalin wasannin makon farko na gasar sun hada da wasan…………
Crystal Palace da Arsenal a Ranar Juma’a 5 ga watan na Agusta.
Sai kuma Ranar Asabar 6 ga watan Agusta
Fulham da Liverpool
Leeds United da Wolverhampton Wanderers
Newcastle United da Nottingham Forest
Tottenham da Southampton
Bournemouth da Aston Villa
Everton da Chelsea
Yayin da Ranar Lahadi 7 ga watan Agusta
Manchester United da Brighton & Hove Albion
Leicester City da Brentford

West Ham United da Manchester City
Sai dai za a yi hutun gasar ta Firimiya a makon ranar 12 da 13, da kuma wasannin da zasu gudana a watan Nuwamba zuwa 26 ga watan Disambar.
Sakamkon gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 da za a gudanar a kasar Qatar.
Kungiyoyin Fulham, da Bournemouth da Nottingham Forest sune cika makin kungiyoyi da zasu kasance 20 da zasu buga gasar ta Firimiya.
Bayan da Burnley, da Watford da kuma Norwich Cit suka fada gasar data gabata.
Wasan farko dai shine zai nuna yadda Arsenal karkashin jagorancin Mikel Arteta’s tayi shirin fara gasar.
Bayan siyan ‘yan wasan Manchester City biyu Gabriel Jesus da kuma Oleksandr Zinchenko, har ma da karin wasu ‘yan wasan kamar Fabio Vieira da Matt Turner da kuma Marquinhos.
Sai kuma Crystal Palace data sayi ‘yan wasa Cheick Doucure da Sam Johnstone da kuma Malcolm Ebiowei.
Haka kuma a karon farko za a fara sauyin ‘yan wasa biyar a gasar ta Firimiya, bayan tin da fari an fara hakan a manyan gasar kasashen turai biyar Bundesliga da Ligue 1 da La Liga da kuma Serie A.