Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniLiverpool ta lashe kofin Community Shield

Liverpool ta lashe kofin Community Shield

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, ta lashe kofin Community Shield bayan do ke Manchester City a wasan karshe.

 

Kungiyoyin biyu sun buga wasan karshe ne a filin Leicester wato King Power a ranar Asabar.

 

Kawo yanzu bayan shafe shekaru 16 Liverpool ta lashe kofin Community shield na shekarar 2022.

 

Dan wasan Liverpool Alexander-Arnold ne ya fara zura kwallon farko a minti na 21.

 

Sai Muhammad Salah ya zura ta biyu a minti na 83, a bugun daga kai sai mai tsaran gida.

 

haka zalika shima sabon dan wasan kungiyar ta Anfiled Darwin Núñez ya zura kwallonsa a minti na 94 dab da zaa kammala wasan.

 

Daga Manchester City kuwa, dan wasan ta J. Álvarez shima ya zura kwallo a minti na 70, amma duk da hakan kungiyarsa ba tayi narasar lashe gasar ba.

 

Yanzu haka Liverpool a kakar wasanni ta bana ta lashe kofin kalu bale na FA Cup, EFL Cup da kuma Community Shield.

 

Sai dai sabon dan wasan da Manchester City ta siya Erling Haaland bai zura kwallo a wasan da ake kallon ya samu damar zura kwallo, amma ya gaza amfani da damar da ya samu a wasan.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...