32.2 C
Kano
Saturday, June 3, 2023
HomeLabaraiWasanniManchester United ta sayi Lisandro Martinez daga Ajax

Manchester United ta sayi Lisandro Martinez daga Ajax

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, ta sayi dan wasan kasar Argentina Lisandro Martinez daga Ajax akan kudi Fam miliyan 57.

Mai shekara 24 tuni ya amince da sanya hannu a kwantaragin shekaru biyar a Old Trafford.

Dan wasan wanda a baya a kungiyar da ya bari ta Ajax ya buga wasanni 120 tin bayan komawarsa daga Defensa y Justicia a shekarar 2019.”

Matuka nasan nayi sa’ar komawa kungiya mai tarihi, wanda nake fatan zan bayar da gudun mawata a tawagar,’ a cewar Martinez.

Dan wasa Martinez ya buga wasa a karkashin jagorancin Ten Hag a lokacin suna Ajax, inda suka lashe gasar Eredivisie ta kasar Holland a kakar wasannin 2021 /2022.

Kuma ya zama gwarzan dan wasa kungiyar ta Ajax a kakar data gabata ta 2021-22.

Kuma dan wasan bayan Martinez ya zama cikin ‘yan wasa uku DA Manchester United ta siya, bayan Tyrell Malacia da Christian Eriksen da ya zo United a matsayin kyauta.

Latest stories