‘Yar wasan mata ta Najeriya Tobi Amusan ta sake lashe zinare a tseren mita 100 na gasar kasashen rainon Ingila wato (Commonwealth) da ke guna a birnin Birmingham na kasar Ingila.
Mai shekara 25 ta lashe zinaren ne a wasan da ta yi a ranar Asabar 6 ga Agustan da muke ciki.
Wannan na zuwa ne bayan da ta zama yar wasan Najeriya ta farko da ta lashe zinare a gudun mita 100 a gasar da ake ci gaba da gudanarwa.
Amusan, wacce ta shafe tarihin duniya a wasan kusa dana karshe, inda ta yi dakika 12.12, ta kuma hau kan layi a filin Hayward a dakika 12.06.
‘Yar kasar Jamaica Britany Anderson ta samu azurfa a dakika 12.23, yayin da zakaran Olympic Jasmine Camacho-Quinn ta Puerto Rico ta samu tagulla a 12.23.
Amusan ta kafa tarihi a duniya a wasan dab da na kusa da na karshe, inda ta karya mafi kyawun dakika 12.20 da Keni Harrison na Amurka ya yi a shekarar 2016.
Tawagar dai na kunshe da ‘yan wasa hudu ta Tobi Amusan, da Rosemary Chukwuma, da Grace Nwokocha da kuma Favour Ofili.
