Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHarin jirgin kasan Kaduna: Gwamnatin Neja za ta kubutar da iyalan tsohon...

Harin jirgin kasan Kaduna: Gwamnatin Neja za ta kubutar da iyalan tsohon gwaman Kano Idris Garba

Date:

Abdurrashid Hussain

Gwamnatin Neja ta fara wani kokari don ganin an ceto mata da ‘ya yan tsohon gwamnan Jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar APC, Janar Idris Garba daga hannun maharan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Sakataren Gwamnatin Neja, Ahmed Ibrahim Matane, ne ya jagoranci tawagar gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello a karshen mako, zuwa gidan tsohon gwamnan Kanon, kuma shugaban Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida.

Ya misalta garkuwa da iyalan har su shida a matsayin abun kaico, in da ya ce harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya kara farkar da gwamantin Neja kan yaki da yan ta’adda.

Ya kuma roki iyalan tsohon gwamnan na Kano, da sauran wadanda aka yi garkuwa da yan uwansu, su kyautatawa gwamnatin zaton cewa za ta yi duk mai yiyuwa wajen ganin sun kubuta daga hannun yan ta’addan.

An dai sace matar tsohon gwamnan Maryam Bobbo, da ‘ya ‘yansa Abubakar da Ibrahim da Fatima da kuma Zainab, yayin harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a watan Aprilun da ya gabata.

Latest stories

Related stories