Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciFasakauri:Kwastam za ta yi gwanjon motoci dubu bakwai

Fasakauri:Kwastam za ta yi gwanjon motoci dubu bakwai

Date:

Abdurrashid Hussain

Hukumar hana fasa kauri ta kasa Custom ta ce za ta yi gwanjon motoci dubu 7 da aka shigo da su kasar nan matukar masu su basu yi musu rijista da sabon tsarin rijistar sabbin ababan hawa ba.

Comptrollan hukumar da ke kula da tashar ruwan Legas Festus Oyedele Okun ne bayyana hakan ranar Litinin, yana mai cewa motocin dubu 7, sun kunshi wanda kirarsu ta yi kasa da shekarar 2013.

Yace za a kwashe motocin zuwa rumbunan ajiyar gwamnatin tarayya a Ikorodun jihar Legas, domin yin gwanjon su, in masu su basu yi rijistar ba nan da watanni uku masu zuwa.

Ya kuma ce za a fara kwashe motocin ne da zarar tashar ta gama tantance jiragen da suka yi dakon su, domin bawa hukumar hana fasa kwaurin damar yin aikinta.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories