Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta haramta adai-dai ta sahu bayan karfe 10:00 na...

Yanzu-yanzu: Gwamnatin Kano ta haramta adai-dai ta sahu bayan karfe 10:00 na dare

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Gwamanatin Kano ta ce daga ranar Alhamis 20 ga Yulin da muke ciki ta harmata sana’ar adai-daita sahu bayan karfe  na10:00 dare a fadin jihar nan.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Kano Malam Muhammadu Garba ya fitar ranar Litinin.

Ya ce an cimma matsayar ne a taron masu ruwa da tsaki kan al’amurna tsaro a jihar nan.

Garaba ya kara da cewa matakin wani bangare ne na ganin an kare lafiya da dukiyoyin al’umma a fadin jihar Kano.

Ya kuma bukaci masu sana’ar a daidaita sahu su bada hadin kai kan wanana doka, a cewarsa jami’an tsaro za su hukunta duk wanda aka kama ya karya dokar.

Latest stories

Related stories