Saurari premier Radio
24.2 C
Kano
Monday, September 9, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiASUU-Kungiyar Kwadago za ta tsunduma yajin aiki

ASUU-Kungiyar Kwadago za ta tsunduma yajin aiki

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kungiyar Kwadago za ta gudanar da zanga-zangar kwanaki biyu a fadin kasar nan domin nuna goyan bayansu ga yajin aikin kungiyoyin malaman jami’o’i na kasa ASUU.

Wanann na kunshe cikin wata sanarwa da shugaban kunigyar Kwamared Ayuba Wabba da sakataren ta Emanuel Ugboaja suka sanyawa hannu.

Sanarwar ta umarci dukkanin manobin kungiyar da ke fadin jihohin kasar nan 36 da birnin tarayya Abuja su fita zanga-zangar don taya ASUU jimamin halin da suke ciki.

Ta ce duka rassan jihohi su shirya gagarumar zanga-zangar a ranakun 26, da 27 ga watan Yulin da muke ciki.

A cewarta wanann jan hankalin gwamnatin tarayya ne, kan ta kammala tattaunawa da kungiyar malaman jami’o’in, domin bude jami’o’in kasar nan.

A jiya ne dai tsohun shugaban kungiyar lauyoyi ta kasa Chif Wole Olanipekun (SAN), ya ce ya kamata a dauki batun yajin aikin malaman jami’o’in kasar a matsayin wani babban al’amari.

Latest stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...

Related stories

Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a 2027 – Kwankwaso

"Ni zan yi nasarar lashe zaben shugaban kasa a...

Mai magana da yawun Tinubu ya ajiye muƙaminsa

Mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan...