27.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabarai2023: Kwankwaso zai kaddamar da Pastor a matsayin mataimakinsa

2023: Kwankwaso zai kaddamar da Pastor a matsayin mataimakinsa

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...
Mukhtar Yahya Usman
A ranar Litinin din nan ne dan takarar shugaban Najeriya na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, zai gabatar da mataimakinsa ga ‘yan kasar.

Wasu hotuna da dan takarar ya wallafa a shafinsa na Facebook sun nuna tsohon gwamnan na Jihar Kano da tawagarsa suna duba babban dakin taro na International Conference Centre da ke Abuja, inda za a gudanar da taron.

A makon jiya ne Sanata Kwankwaso ya Fasto Idahosa, dan asalin Jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya, a matsayin mutumin da zai yi masa mataimaki a zaben 2023.

Faston, wanda fitaccen mawakin bushara ne, ya taɓa samun lambar yabo ta Majalisar Dinkin Duniya a matsayin jakadan zaman lafiya, saboda gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban bil adama da zaman lafiya ta hanyar wa’azinsa.

Ya fitar da kundi uku na jerin waƙoƙin bushara a baya.

Bishop Isaac Idahosa shi ne shugaba, kuma babban Fasto na cocin God First Ministry, wadda aka fi sani da Illumination Assembly, da ke Lekki Ajah, a jihar Legas.

Cocin da ya kafa sama da shekaru 25 da suka gabata.

Latest stories