Hafsat Iliyasa Dambo
Masarautar garin Yantodo dake karamar hukumar Tsafen jihar Zamfara ta shirya tsaf domin nada kasurgumin dan ta’addar nan da ake kira Adamu Aleru a matsayin Sarkin Fulani na Masarautar a yau.
Matakin nada Aleru a matsayin basarake ya biyo bayan tattaunawa tsakanin dattawan masarautar da shugaban ta’addancin.
Wasu majiyoyi a gundumar da suka nemi a sakaya sunansu saboda dalilai na tsaro sun shaida wa manema labarai cewa an yanke shawarar nada shi ne domin samar da zaman lafiya a Masarautar Tsafe da ‘Yandoton Daji da ke fama da rikici da sauran yankunan Zamfara da Katsina.
Daliban makarantu gwamnati a jihar Zamfara ba zasu rubuta WAEC ba.
Da yake tabbatar da labarin nadin ga premier radio, wakilin masarautar Magaji Lawal ya musanta cewa Adamu Aleru dan ta’adda ne.
A cewar shi masarautar bata da masaniyar Adamu Aleru yana da wata alaka da ta’addanci.
Matsalar tsaro:Malisar wakilai ta yi barazanar tafiya yajin aiki
Idan dai za a iya tunawa, tun a shekarar 2019, Adamu Alero ya shiga cikin jerin yan taaddan da gwamnatin jihar katsina ke nema ruwa a jallo saboda wasu hare hare da ake zargin shi da tawagarsa suka kaddamar a wasu yankunan jihar.