33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiMamakon ruwan sama ya kashe mutum shida, ya jikkata 60 a Jigawa

Mamakon ruwan sama ya kashe mutum shida, ya jikkata 60 a Jigawa

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

 

Mukhtar Yahya Usman

A kalla mutane shida ne suka mutu, wasu 60 suka jikkata, sakamakon mamakon ruwan sama da iska mai karfin a jihar Jigawa.

Al’amarin ya faru ne a daren Talatar nan a karamar hukumar Kafin Hausa.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Muhammad Samin Yahya ne ya bayyana adadin, bayan da ya ziyarci wadanda lamarin ya shafa a babban Asibitin karamar hukumar.

Ya ce al’amarin ya faru ne cikin daren jiya Talata yayin da mutanen ke kwance cikin gidajensu ake kuma ta tsala ruwa.

Ya ce ruwan ya kashe shida, sama da sittin suka jikkata, yayin da aka yi asarar dukiya ta milyoyin kudi.

“Kawo yazu dai munyi asarar mutum shida, kimanin 60 suka jikkata, sai kuma dukiya mai yawa da ta salwanta” a cewarsa.

Ya kara da cewa wadanda suka jikkata suna asibiti suna karbar magani yayinda wadanda suka mutu aka yi jana’izarsu

Latest stories