Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Tuesday, April 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda aka baiwa alhazan kasar nan gurbataccen abinci a saudiyya

Yadda aka baiwa alhazan kasar nan gurbataccen abinci a saudiyya

Date:

Mukhtar Yahya Usman
Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta ce za ta bi kadin hakkin alhazan kasar nan da aka baiwa gurbataccen abinci a kasa mai tsarki.

Shugaban hukumar Zikirulla Kunle ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba daga kasar Saudiyya.

Kunle ya ce za su nemi hukumomin kasar ta Saudiyya su dawo mata da kudin abincin da ta biya saboda baiwa mahajjatan kasar nan gurbataccen abincin.

Ya ce tuni suka rubuta wasika zuwa ga hukumomin Saudiyya da suka kamata kan yanayin abincin da aka ba alhazan wanda suka yi ta korafi a kan ingancinsa.

Rashin abinci mai kyau dai na daya daga cikin tarin matsalolin da suka yi wa alhazan Najeriya katutu yayin aiki Hajjin na bana.

A cewar Zikrullah, an sami matsalar abincin a Muna ne saboda hukumomin Saudiyya ne suka karbe ragamar ciyar da alhazan, sabanin yadda ake yi a baya.

Shugaban ya kuma yaba wa alhazan kan hakuri da fahimtar da suka nuna duk da tarin kalubalen, yana mai cewa Aikin Hajji dama ya gaji jarabawa iri-iri.

Daga nan sai ya hore su da su ci gaba da kasancewa jakadun Najeriya na gari, a ragowar lokacin da ya rage musu a can.

Latest stories

Related stories