Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaRushewar gina ya hallaka mutum biyu a Kano

Rushewar gina ya hallaka mutum biyu a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Wasu yara biyu almajirai sun rasa ransu, wasu uku suka jikkata bayan da gini ya rufto musu a unguwar Hotoron gabas dake karamar hukumar Nasarawa.

Hadarin ya faru ne da misalin 3:00 na daren jiya Juma’a.

Shaidun gani da ido sunce wani gini ne da aka fara ba a kammalaba, almajiran ke shiga ciki suma kwana.

Sunce lokacin da ginin ya rufta akwai almajirai biyar suna bacci da hakan yayi sanadiyyar mutuwar biyu daga ciki.

Haka zalika ragowar ukun suna cikin mawuyacin hali.

Tuni dai aka yi jana’izar wadanda suka mutun Kamar yadda addinin musuluncin ya tanada.

Har yanzu hukumar kashe gobara ta jihar Kano bata magantu kan al’amarin ba, duk da kokarin da mukayi na jin ta bakinsu.

Latest stories

Related stories