Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasar saudiyya ta gindaya sharudan aikin Hajjin bana

Kasar saudiyya ta gindaya sharudan aikin Hajjin bana

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Kasar Saudiyya ta gindaya sharrudda ga wadanda za su gudanar da aikin hajjin bana.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da ma’aikatar aikin hajji da umra ta kasar ta fitar ranar Asabar.

Sharuddan sun hadar da bin matakan kare kai daga annubar Covid-19, wadda ita ta hana gudanar da ibadar a Shekarun 2020 da 2021.

Haka kuma duk wanda ya haura shekaru 65 ba zai gudanar da aikin hajjin ba.

Sannan duk wanda zai shiga kasar sai an yi masa gwajin Corona aƙalla kwanaki biyu kafin shigarsa.

Sanarwa ta kara da cewa dole ne duk maniyyata aikin hajji bana a yi musu allurar rigakafin Covid-19 wadda kasar Saudiyya ta amince da ita.
Sai kuma bin sauran matakan kula da Lafiya kamar yadda aka saba.

Haka kuma kasar ta ce mutane Milyan daya ne za su gudanar da aikin hajjin na bana.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories