Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai2023:Osibanjo ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa

2023:Osibanjo ya bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

Mataimakin shugaban Kasa Farfesa Yemi Osibanjo ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a kakar zaben shekarar 2023 mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne a yau litinin a cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a internet.

Osibanjo yace idan ya sami damar zama shugaban kasa zai tabbtar da gyara matsalolin tsaro da fannin shari’a da kuma tabbatar da adalci ga kowa.

Osibanjo yace zai tabbatar da kyakykyawan tsarin tattalin arzikin Najeriya da walwalar yan kasa da zarar ya sami dama.

Ya kuma ce zai tabbatar da karasa tsarin gwamnatin tarayya da ta fara na fidda yan Najeriya miliyan 100 da ga kangin talauci.

A jawabin na mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo ya nemi goyan bayan yan Najeriya duba da irin kwarewar da yace yana da ita a sha’anin mulki.

Osibanjo a yanzu shima ya shiga sahun yan siyasa a kasar nan da suka nuna sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasa.

Wandanda suka ayyanna takararsu

A baya-bayannan dai wasu yan siyasa sun bayyana aniyar tsayawa takarar shugabancin kasar nan a kakar Zabe ta 2023 mai zuwa.

Daga cikin wadanda suka bayyana aniyarsu yazuwa yanzu akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Alh. Atiku Abubakar sai tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ministan sufuri Rotimi Amaechi.

Haka kuma jagoran jam’iyyar APC na kasa Bola Ahmed Tinubu  shima tuni ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya.

Shima gwamnan Ebonyi David Umahi da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello dukkaninsu sun bayyana aniyar tsayawa takarar a zaben 2023 mai zuwa.

To saidai kaddamar da aniyar tsayawa takarar da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjon yayi a yau litinin, ana hasashen ka’iya kawo wani sabon yanayi a jam’iyyar APC, duba da yadda ake ganin yanada tasiri kasancewarsa lamba na 2 a mulkin wanann kasa a halin yanzu.

Latest stories

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...

Related stories

Gwamnatin Sokoto tayi martani ga mataimakin shugaban ƙasa.

Gwamnatin Sakkwato ta yi martani ga Mataimakin Shugaban Kasa...