33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiDamfara:Kotu ta bada umarnin sake gurfanar da A A Zaura

Damfara:Kotu ta bada umarnin sake gurfanar da A A Zaura

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...
Kotun daukaka kara a Kano ta bada umarnin a sake gurfanar da dan takarar gwamnan Kano Abdulkarim A Zaura bisa zargin damfara.

Idan za a iya tunawa dai wata babbar kotun jihar Kano ce ta wanke A A Zauran daga dukkanin tuhume-tuhumen da ake masa.

Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi kan zarge zarge 5 a gaban babbar kotun tarayya dake Kano.

Hukumar ta zargi shi da damfarar wani dan kasar Kuwait kudi har Dala Miliyan 1 da dubu dari uku da 20 bisa batun cewa yana harkallar gina gidaje a Dubai da Kuwait da sauran kasashen larabawa.

A ranar 9 ga watan Yuni na shekarar 2020, mai shari’a Lewis Allagoa ya wanke A A Zaura daga zargin.

Sai dai lauyan masu kara ya daukaka kara kan hukuncin.

A hukuncin kotun daukaka karar mai alkalai 3 ta yi watsi da hukuncin babbar kotun Inda ta yi umarni a sake gurfanar da shi a gaban wata kotun.

Latest stories