Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoAn gano yara 4 da aka sace daga Kano aka sayar a...

An gano yara 4 da aka sace daga Kano aka sayar a Kudu

Date:

Mukhtar Yahya Usman

An sake gano wasu yara hudu cikin yaran Kano da aka sace aka sayar da su a jihar Anambra, da wasu yankunan Kudu.

Shugaban kwamitin da gwamnati ta kafa domin gano yaran justice Wada Umar Rano ne ya sanar da hakan lokacin da yake Mika yaran ga gwamnatin Kano.

Justice Rano  ya ce an gano yaran ne a jihar Lagos da taimakon jami’an tsoron farin kaya DSS.

Sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya karbi yaran a ofishinsa a jiya Juma’a.

Yaran sun haɗa da Abdullahi Yahaya mai shekara 14, Umar Sani,12, Isma’ila Sabo, 12, da Isah Haruna mai shekara 13.

Alhaji Wada ya ce bayan da aka gano yaran ne aka yi musu gwajin halitta na DNA domin tabbatar da iyayensu.

Haka kuma gywajin na DNA ya tabbar da cewa wadanda ke rike da su  ba ‘ya’yansu bane.

Ya kara da cewa an danka ukun da aka gano iyayen a hannun mahaifansu, yayin da ake neman iyayen ragowar dayan.

Idan za a iya tunawa dai tun a shekarar 2019 aka gano wasu yara 9 da a ka sace a ka sayar a jihar Anambra.

Galibin yaran dai an sauya musu addinin da suna zuwa na yankin Kudu.

Hakazalika iyayen yara na fadin cewa yanzu haka a kwai yara sama da 100 da ba a gan su ba.

Latest stories

Related stories