Saurari premier Radio
26.4 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin manoma da makiyaya: An kashe mutum 6 a Jigawa

Rikicin manoma da makiyaya: An kashe mutum 6 a Jigawa

Date:

Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma ya yi sanadin kisan mutum shida tare da jikkata wasu a garin Magiram na Karamar Hukumar Guri ta jihar Jigawa.

Rahotanni daga yankin sun ce rikicin wanda ya faro tun kwanakin baya ya kazance ne ranar Juma’a, inda ya kai ga mutuwar mutanen.

Rundunar ’Yan Sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, kodayake ta ce mutum biyu ne kawai suka mutu, wasu biyar kuma suka ji raunuka.

Kakakin Rundunar, ASP Lawal Shisu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa ranar Juma’a, inda ya ce tuni aka cafke mutum biyu, yayin da ake ci gaba da farautar sauran.

Sai dai ya ce an garzaya da ragowar Babban Asibitin garin Hadejia, inda suke samun kulawa.

Kakakin ya kuma ce suna nan suna ci gaba da farautar ragowar mutanen don tabbatar da sun shiga hannu.

ASP Lawal ya ce a ranar Juma’a ce rundunar ta samu rahoton rikicin tsakanin bangarorin biyu.

“Nan da nan muka aike da jami’anmu. Suna zuwa suka iske gawar mutum biyu; ta wani mai suna Umar Abdul Rahusa mai kimanin shekara 35 da kuma wani wanda ba a kai ga tantance shi ba.

” Mun kuma ceto mutum biyar da suka jikkata, kuma an garzaya da su Babban Asibitin Hadejia,” inji kakakin.

Haka kuma kakakin ya tabbatar da cewa hankula sun fara kwanciya bayan jami’ansu sun dawo da doka da oda a yankin, inda ya shawarci mazauna garin su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...