Saurari premier Radio
25.1 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRIKICIN APC: Yadda tsagin El-Rufa'i ya tabe

RIKICIN APC: Yadda tsagin El-Rufa’i ya tabe

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Yayin da al’amura suka dauki dumi a jam’iyyar APC a iya cewa yunkurin bangaren Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na hambarar Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni daga kujerar shugabancin rikon jam’iyyar APC ya tashi a tutar babu.

Sanya bakin da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi cewa ita Buni ta sani a matsayin shugaban rikon APC, da kuma umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa kada a taba kujerar Buni ta jagorantar jam’iyyar sun yi ciksa ga masu son tsige shi daga kujerarsa.

Kawo yanzu, Buni, wanda tun a watan Yunin 2020 yake jagorantar APC, ya tsallake duk tuggun da bangaren El-Rufai ya shirya na ganin shugabancin jam’iyyar ta fita daga hannunsa.

Gwamnan Jihar Kogi, Yahya Bello da Gwamna Hope Uzodinma na Jihar Imo da kuma David Umahi na Jihar Ebonyi su ne suka tsaya kai da fata wajen kare Mai Mala Buni, wanda shi ne Gwamnan Jihar Yobe.

Su kuma El-Rufai da Gwamnan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu da kuma Gwamnan Neja su ne kan gaba wajen neman kawar da Mai Mala Buni.

Yunkurin ya dauki zafi ne bayan tafiyar Buni zuwa birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) domin duba lafiyarsa.

A lokacin ne El-Rufai ya yi ikirarin cewa Shugaba Buhari ya ba wa gwamnonin jam’iyyar umarnin tsige Buni su nada Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya maye gurbinsa.

Sai dai kuma tun bayan hawan Gwamna Bello kujerar a matsayin mukaddashin Buni, kura ta ki lafawa a hedikwatar jam’iyyar.

Buhari ne ya sa mu —El-Rufai

A hirarsa da shirin ‘Politics Today’ na gidan talabijin na Channels, El-Rufai ya bayyana cewa Buhari ne ya ba su ikon tsige Mai Mala Buni daga shugabacin rikon APC.

El-Rufa’i wanda ya zargi gwamnonin APC da zura ido har abubuwa suka dagule a jam’iyyar ya ce gwamnoni 19 da wani mataimakin gwamna daya na jam’iyyar sun yi ittifakin awaitar da umarnin na Buhari.

A cewarsa, ragowar gwamnoni ukun ne suka yi ta baza jita jitar cewa ba a tsige Buni ba.

Shi ma a nasa bangare, Gwamna Akeredolu na Jihar Ondo ya bayyana gwamnonin da ke goyon bayan bangaren Buni a matsayin ’yan damfara.

A wata sanarwa da ya fitar, Akeredolu ya zargi Buni da sanya APC a aljihunsa da kuma kokarin yi wa manufar Buhari burum-

“Ba sai na yi dogon bita ba game da mummunar turbar da Gwamna Mai Mala Buni, tsohon shugaban rikon jam’iyyar, ya yi ba, wanda abin takaici ne ga jam’iyyar.”

Martanim bangaren Buni:

Amma gwamnonin bangaren Buni irin su David Umahi na Jihar Ebonyi, sun yi fito-na-fito da bangaren na El-Rufai, inda shi, Umaru ya kekashi kasa cewa babu wanda ya isa ya tsige Buni.

Umahi ya kuma bayyana cewa Buni ya sa Gwamna Bello na Jihar Neja ne kawai ya zama mukaddashinsa kafin ya dawo daga duba lafiyarsa a Dubai.

Ya shaida wa magoya bayan jam’iyyar APC a Abakalili, hedikwatar Jihar Ebonyi, cewa “Shugaban rikon jam’iyya ya je duba lafiyarsa ne a kasar waje kuma muna nan a lokacin da ya sa Gwamnan Neja ya zama mukaddashinsa.

“Idan har za a yi wani canji a jam’iyya za a sanar da ku, amma a halin yanzu babu wani sauyi da aka yi kuma babu wata baraka a jam’iyyar.”

Wasikar Buni

Daga baya Buni ya fitar da wata sanarwa cewa zai dawo daga ganin likita ya ci gaba da jan ragamar jam’iyyar.

Ya kuma bayyana cewa ya ba wa Gwamnan Neja wasikar zama mukaddashinsa har sai ya dawo gida.

Tuni dai Mai Mala Buni ya dawo ya karbi shugabancin Jam’iyyar da masana ke ganin wannan babban koma baya ne ga bangaren gwamna Nasir El-Rufa’i.

Ko da dai har yanzu tsugunnen ba ta kare al’umma sun zuba idanu domin ganin yadda za ta kaya a babban zaben Jam’iyyar da ke tafe.

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...