Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, April 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu:Akwai yiwuwar bada belin Sheikh Abdulljabbar Kabara

Kotu:Akwai yiwuwar bada belin Sheikh Abdulljabbar Kabara

Date:

Abubakar Haurna Galadanci
Babbar Kotun Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a Jihar Kano ta sanya 31 ga watan Maris, 2022 a matsayin ranar yanke hukunci a kan bukatar ba da belin Sheikh Abduljabbar Kabara da lauyansa ya gabatar mata.

Ana zargin Abduljabbar Kabara ne dai da laifin yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma tayar da hankalin jama’a.

Dayake gabatar da bukatar belin, lauyan malamin ya yi wa kotu alkawarin cewa za su bi dukkanin sharuddan da za a gindaya musu.

Sai dai lauyoyin masu shigar da kara karkashin jagorancin Barista Saida Suraj sun nemi kotu ta yi watsi da bukatar bisa la’akari da girman laifin da ake tuhumar wanda ake zargi, wanda a cewarsu zai iya kai ga yanke mishi hukuncin kisa, karkashin dokar Kundin laifufuka ta Jihar Kano  ACJL 171 (1).

“Baya ga haka kuma, a yanzu da ake gabar kariya babu wani dalili da zai sa a nemi belin wanda ake kara; Haka kuma ba mu ji an ambaci wani dalili mai karfi da zai sa a bayar da  belin ba.” inji shi.
Shi kuwa lauyan wanda ake kara, cewa ya yi kotu tana da hurumin bayar da belin wanda ake zargi kasancewar har yanzu ba ta kama wanda ake zargi da laifin ba, dogaro da sashe na 36 (6) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Hakan ya sa alkalin kotun, Mai Shari’a Abdullahi Sani Sarki Yola ya dage zaman da mako biyu, zuwa ranar 31 ga watan Maris don jin ra’ayin kotun game da batun bayar da belin

Latest stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Related stories

Dan Ganduje ya kai wa Muhuyi ziyarar goyan bayan a binciki mahaifansa

Dan tsohon gwamnan Kano, Abdulaziz Abdullahi Ganduje, ya kai...

Farashin Dizel ya koma 1000 a Najeriya

Rahotanni sun bayyana matatar mai ta Dangote ta sanar...