Saurari premier Radio
36 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYanzu-yanzu: PDP ta bukaci a rushe shugabacinta a Kano

Yanzu-yanzu: PDP ta bukaci a rushe shugabacinta a Kano

Date:

Mukhtar Yahya Usman

Jam’iyyar PDP tsagin Aminu Wali, ta bukaci a rushe shugabancin jamiyyar na jihar Kano.

Wannan na zuwa ne a wani taron gaggawa da uwar jam’iyyar ta kasa ta gudanar tare da dukkanin bangarorinta a Abuja ranar Alhami.

Tsagin Aminu Wali ya ce a yanzu jam’iyyar na cikin wani hali, la’akari da yadda tsagin Kwankwasiyya ke neman hada shugabanci jam’iyyar da kuma wandda yake son komawa ta NNPP.

Sai dai da yake mayar da martani kan batun Bashir Sanata da ke zaman mai Magana da yawun jam’iyyar tsagin Kwankwasiyya ya ce tsagin bai aminta a matakin ba.

A zarge-zargen da tsagin Kwnakwasiyyar ya yi ya ce shima tsagin Aminu Walin ya yi Anti-party inda suka bi Ganduje, harma Gandujen ya basu kwamishina.

Sai dai bayan da uwar jam’iyyar ta kamnala sauraronsu, ta ce za ta duba bukatun dukkanin bangarorin za ta yiwa kowa adalici.

Idan za a iya tunawa a karshen watan da muke ciki ne jagoran jam’iyyar tsagin Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya sha alwashin sauya sheka zuwa NNPP, kamar yadda BBC ta ruwaito a baya.

Kwankwason yace ya soma daukar matakan nesanta kansa daga sha’anin jam’iiyar ne don ganin ko masu ruwa da tsakinta zasu nemi jin koke koken da suke dashi.

Latest stories

Related stories