Saurari premier Radio
41.5 C
Kano
Tuesday, April 30, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin APC: Banza bakwai ta shuka dusa -Ganduje

Rikicin APC: Banza bakwai ta shuka dusa -Ganduje

Date:

Jim kadan bayan samun nasarar da tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi a Gaban kotu gwamnan yayi zazzafan martani irin na siyasa.

Gwamna Ganduje yace a yayin da wasu suke shuka iri, wasu sun shuka dusa.

Ya kuma kara da cewa “Banza bakwai ta shuka dusa”

Wannan kalamai na gwamna Ganduje ana ganin zasu bude wani sabon babi na siyasa a jihar Kano a daidai lokacin da ake kokatin yin sulhu tsakanin Tsagin Shekarau da Gandujen.

A yau ne dai kotun daukaka kara tayi watsi da hukuncin kotun da ta tabbatarwa da tsagin Sanata Malam Ibrahim Shekarau nasara, inda kotu tace kotun da tayi hukunci a baya bata da hurumin yin wannan hukunci.

Latest stories

Kotu ta ɗage shari’ar zargin tsohon gwamna Ganduje.

Babbar kotun jihar Kano ta dage shari’ar zargin tsohon...

A mahaifata sai da izinin ƴan bindiga muke noma-Attahiru Bafarawa.

Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koka...

Related stories