Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZamfara: An kama mutane 3 da jabun kudi na naira miliyan 2

Zamfara: An kama mutane 3 da jabun kudi na naira miliyan 2

Date:

 

Hukumar tsaron farin kaya ta Civil Defence a jihar Zamafara ta kama mutane uku da jabun kudi na naira miliyan 2.

 

Kakakin hukumar Ikor Uche, ne ya shaida hakan inda ya ce jami’ansu sun kama mutanen ‘yan asalin karamar hukumar Tsafe a Gusau, suna kokarin biyan kudin adaidaita sahu da kudin jabu.

 

A cewar sa, bayan gudanar da bincike sun gano cewa daya daga cikin mutane ukun ya fara tu’ammali da kudin jabun tun a shekarar data gabata.

 

Kwamandan hukumar, Muhammad Muazu,ya shawarci aľummar jihar da su cigaba da sa ido tare da sanar da duk wani motsi da basu gamsu da shi ba ga jami’an tsaro.

 

Yace kuma hukumar zata damka masu laifin qa hukumomin da suka dace domin daukar matakin daya kamata.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...