Saurari premier Radio
41.8 C
Kano
Wednesday, May 1, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAbubuwa 4 da ‘yan kabilar Igbo suke so Tinubu ya yi musu

Abubuwa 4 da ‘yan kabilar Igbo suke so Tinubu ya yi musu

Date:

Kungiya ‘yan kabilar Igbo ta Onanaeze, ta mika wa zababben shugaban kasa Bola Anmed Tinubu sharuda hudu, wadanda sai ya amince da su kungiyar za ta mara masa baya.

 

Babban sakataren kungiyar na kasa, Okechukwu Isiguzoro, ya ce suna so sabon shugaban kasa ya sako Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar da ke rajin kafa kafa ‘yantacciyar kasar Biafara ta IPOB, wanda hakan zai taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a yankin kudu maso gabas.

 

Haka zalika kungiyar ta kuma ya ce, ya kamata Tinubu ya tabbatar da cewa an samar da shugaban majalisar dattijan daga yankin Kudu maso Gabas.

 

A cewar Onanaeze, ya kamata sabon zababben shugaban, da zarar ya karbi ragamar mulki, ya tabbatar da cewa an sarmar da jihohi a kalla guda shida, daga yankin Kudu maso gabashin Najeriyar.

 

Kungiyar ta bukaci zababben shugaban ya tabbatar da cewa, an samar da tsare-tsaren da za su habaka tattalin arzikin yankunan ‘yan kabilar Igbo, a kuma bude tashar jiragen ruwa ta Calabar, sannan a tsaftace kogin Azumiri da ke jihar Abia, hadi da yiwa yan kungiyar IPOB afuwa, sannan kuma a biya diyya ga  iyalan wadanda aka kashe.

 

Latest stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...

Related stories

Netanyahu ya nanata ƙudirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta ƙasa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...