Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Wednesday, April 24, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciFashola ya bada tabbacin kammala titin Legas-Ibadan, Abuja-Kano

Fashola ya bada tabbacin kammala titin Legas-Ibadan, Abuja-Kano

Date:

Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya ce za a kammala titin Legas-Ibadan da Abuja zuwa Kano a karshen watan Afrilu.

 

Fashola ya bayyana haka ne a wani yayin da yake duba aikin gadar Loko-Oweto dake jihar Nasarawa, wadda tuni aka kamala.

 

Ministan ya bukaci masu amfani da hanyar Legas zuwa Ibadan da su yi hakuri, yana mai cewa ana yin duk mai yiwuwa don ganin an kammala aikin.

 

A cewar ministan “Aiki ne mai wahala a iya aiwatarwa, domin kuwa yana daga cikin manyan tinunan kasar nan, don haka dole a tsaya a yi aiki mai kyau.

 

Dangane da aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano, Fashola ya ce shi ne aikin titin mafi girma ta fuskar kasafin kudi.

 

Ya kara da cewa an samu gagarumin ci gaba a tsakanin Zariya da Kano, wanda ya kai kimanin kilomita 137.

 

Ministan ya ci gaba da cewa za a bude bangaren hanyar Kaduna zuwa Zariya da aka rufe a karshen watan da muke ciki.

 

Sai dai ya bayyana cewa bangaren hanyar Kaduna zuwa Abuja ya samu tsaiko saboda matsalar tsaro.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...