
Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar ICEADA da hadin gwiwar kugiyar Big Dream sun gudanar da bita ga masu horas da kungiyoyin kwallon kafa a jihar Kano.
An gundar taron bitar tare da horas da su dabarun da zasu inganta aikin horas da kwallon kafa wajen rage zaman banza da dakile shaye-shaye a tsakanin matasa.
Da yake jawabi shugaban kungiyar ICEADA, Farfesa Muhammad Bello Shitu ya ce zasu dauki nauyin daya daga cikin kwaca-kwacai a jihar Kano zuwa makarantar horas da kwallon kafa ta kasa domin kara samun kwarewa da da shaidar kocin wasanni a ko ina a kasar nan.
A nasa bangaren shugaban gamayyar kungiyoyin ilimi na jihar Kano Dakta Auwalu Halilu, ya ce irin wannan horo zai taimaka wajen inganta harkokin wasanni a jihar Kano.
Ya ce irin wannan tsarin shi ake gudanarwa a kasashen duniya ta hanyar koyar da abubuwan da ya kamata ayi a rubuce bayaga aiwatar da aikin a aikace.
Ya ce irin wannan bita zata baiwa kwaca-kwacan damar kara fahimtar sana’ar da tare da yin gogayya da takwarorinsu na wasu kasashen.
Shima wani daga cikin mai horas da kwallon kafa a nan Kano Sa’ad Ahmad Ma’aji (Coach Amo) mai horos da kungiyar kwallon kafa ta Kano Lines ya ce masu horas da kungiyoyin wasanni a jihar Kano sun dade suna bukatar irin wannan bita.
Ya ce akwai bukatar hukumomin wasanni da kungiyoyi su rinka tallafawa ta hanyar bayar da horo domin inganta harkokin wasanni musamman a yankunan karkara da rage zaman banza a tsakanin matasa.
Taron ya samu halartar kwararru da malamai a bagaren wasanni inda suka gabatar da darussa daban daban na inganta aikin horos da kwallon kafa a jihar Kano.
